Jirgin Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba da aiki.

Ranar 23 ga wannan watan na mayu da muke ciki ne dai ranar da aka sanya na ci gaba da zirga zirgar jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna da Abuja.

A wata sanarwa ga manema labarai daga hukumar jiragen kasa ta kasa wato Nigerian Railway Corporation mai sanya hannun kakakin hukumar Yakubu Mahmood ta fitar ,hukumar ta jiragen kasa ta ce yanke hukuncin ci gaba da zirga zirgar jiragen kasa ba ya na nufin an jingine kokarin da ake yi na karbo mutanen da ‘yan bindiga suka kwashe daga jirgin da aka kaiwa hari a watan Maris din da ya gabata ba.

Hukumar ta jiragen kasa dai ta bada tabbacin bada kariya da kuma tsaro ga fasinjojin wannan jirgi ,inda sanarwar ta ce gwamnati  ba za ta bada kai ga wata baraza daga wani gungun ‘yan taadda ba. To sai dai Kusan dukkan wadanda aka kwashe a wannan jirgi dai har yanzu suna hannun ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Ansaru ne,masu kama da boko haramun a tsari da ayyukan su,wadanda aka bayyana cewa sun rike mutanen ne domin ayi misayi da shugabannin su da masu daukar nauyin su dake hannun hukuma.

A kwanan baya kadan dai gwamnan jahar Mal Nasiru El Rufai ya nuna damuwa a bisa yadda sojojin Najeriya suka ki bin shawarar sa ta shiga dazuzzukan da ‘yan taadda ke buya ayi ta ta kare.

Leave a comment