Sanata Mal. Uba Sani ya lashe zaben fid da gwani a Kaduna.

Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Mallam.Uba Sani ya sami gagarumar nasara a zaben fid da gwani na jamiyyar APC na mukamin gwamna a jahar Kaduna.

Sanata Uba Sani ya sami wannan nasara ne bayan da ya sami kuri,u 1,149, a yayin da Bashir Abubakar ya sami kuri,u 37, Sani Shaaban kuma ya tashi da kuri’u 10 kacal.

A jawabin amincewa da wannan nasara, Sanata Uba Sani ya mika godiyar sa ga shugabannin jamiyyar APC na jahar Kaduna da kasa baki daya, gwamnan jahar Kaduna Mal.Nasiru El Rufai, ‘ya’yan jamiyyar APC da sauran jama,ar jahar Kaduna inda yayi alkawarin jajircewa domin ganin yayi aiki tukuru don ci gaban jahar Kaduna baki daya.

Dama dai Sanata Mallam Uba Sani shine wanda gwamnan jahar Kaduna Mallam Nasiru El Rufai ya amincewa tsayawa takara a jamiyyar APC.

Leave a comment